Thursday, 7 September 2017

Yadda Mata suke Hukunta Mazajensu A Legas



 Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce tana samun karin rahotannin da ke nuna mata na lakadawa mazajensu duka a jihar.
Kwamishinan shari'a na jihar Mr Adeneji Kazeem ya ce sun samu rahotanni da dama daga wurin mazajen da ke shan dan banzan duka daga wurin matansu, yana mai bayyana lamarin da cewa ya yi muni.
Ita ma shugabar hukumar yaki da cin zarafin mutane ta jihar, Misis Lola Adeniyi, ta shaida wa BBC cewa, "Ma'aurata maza 55 sun kawo karar matansu inda suke zargin sanya su cikin halin damuwa da furta bakaken maganganu da kuma lakada musu duka".
"Akwai uku da suka ce matansu sun yi musu dukan kawo-wuka, biyu daga cikinsu sun ce suna da shaida hotuna da ke nuna hakan; da yawa daga cikinsu suna so hukuma ta warware matsalolin ba tare da an kai kararsu a gaban kotu ba. Wasu mazajen kuma suna so ne a kai su asibit domin yi musu magani", in ji shugabar
Ba kasafai dai ake samun labarin kan yadda mata ke dukan maza ba.
Sai dai wata mata ta shaida wa BBC cewa tura ce ta kai bango shi ya sa muke yin raddi.
Ta kara da cewa, "Babu mamaki cin zarafin da maza ke yi wa mata a gida ne ya yi yawa shi ya sa matan su ma suke lakadawa mazajensu nasu duka. Ka san idan tura ta kai bango ba ka da mafita idan baka tashi ka kare kanka ba".

Yaki da Chin Hanci da Rashawa a Nigeria Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu


Ko Yanzu Alhamdulillah Gwamnatin Nigeria Karkashin Jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Tayi Nasara a Bangaren Yaki da Chin Hanci da Rashawa

Saboda An Wayi Gari a Kasa Irin Nigeria An Samu Kudi an Rasa Mai Su Kowa Na Tsoron Yace Nashi Ne Domin Gudun Hushin Hukuma Wanda A Yan Shekarunan Bamu Taba Tsammanin Haka Zata Faruba

Sai Dai Muyi Godiya Ga Allah Mu Roki Allah Yakara Taimakon Wanan Gwamnatin Wajen Dawo Da Martaban Kasarmu Nigeria

Daga

Aliyu Abdullahi Malumfashi

Wednesday, 6 September 2017

Zai Dauki Lokaci Kafin Talakawa Su Fara Amfana Da Farfadowar Tattalin Arziki - NBS


Shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa ( NBS), Yemi Kale ya yi karin haske game da rahoton da hukumar ta fitar na Farfadowar tattalin arzikin kasa daga kariyar da ya yi inda ya nuna cewa zai dauki lokaci kafin farashin kayayyaki su sauko kasa don amfani talakawa.

Ya ce, fita daga kariyar tattalin arziki su ne matakin farko na kai wa ga samun sauki kuma dole dai dore a kan haka sannan za a kai ga nasara tare kuma da kauce sake komawa gidan jiya.

YADDA SAMA DA MUSULMAI DUBU TALATIN SUKAYI HIJIRA CIKIN KANKANIN LOKACI DAGA BURMA



DAGA AUWAL M KURA
Kasa da awanni ashirin da hudu al-ummar Rohingya kusan Dubu Talatin da bakwai (37,000) suka tsere zuwa Bangladesh
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla musulmai ‘yan
Kabilar Rohingya dubu talatin da Bakwai ne, (37,000) suka tsere zuwa kasar Bangladesh cikin Awanni ashirin da hudu24 bayan irin kisar girlar da akeyi musu a kasar Burma
Inda majalisar dinkin duniya ta Bayyana  lamarin da matsayin Gudun hijira mafi girma da aka Taba gani cikin karamin lokaci Tun bayan sabon tashin Hankalin da ya barke a kasar Myanmar .
A cewar Majalisar, wannan ta sa Yawan ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere daga  burma zuwa Bangladesh ya karu zuwa dubu Dari da ashirin da biyar (125,000) daga dubu Casa’in (90,000)

A Karo Na Biyu Buhari Ya Soke Zaman Majalisar Ministoci



A karo na biyu tun bayan da ya dawo jinya daga waje, Shugaba Muhammad Buhari ya soke zaman majalisar ministoci wanda aka tsara gudanarwa a yau Laraba.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya ce an soke zaman majalisar ce saboda rashin isasshen lokaci da ministocin za su nazari kan batutuwan da aka tsara tattaunawa a lokacin zaman sakamakon bukukuwan Babban sallah da aka gudanar.

2019: Ministar Harkokin Mata Ta Fara Yi Wa Atiku Kamfe


Ministar harkokin mata, Hajiya Aishatu Isma'ila ta soma yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yakin neman zabe na shekarar 2019. Ministar, wacce ta jagoranci shugabannin jam'iyyar APC na jihar Taraba domin kai gaisuwar Sallah ga Atiku Abubakar, ta yi addu'ar Allah ya ba shi shugabancin kasar a 2019.

Wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian wacce ake wallafawa a shafin intanet ta buga, ya nuna ministar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasar tana cewa, "Your Excellency (mai girma), babanmu, shugaban kasarmu idan Allah ya yarda a shekarar 2019... a gabanka, mutanenka ne, magoya bayanka har abada; mutanen jihar Taraba.

"Sun zo gaisuwar ban-girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna ta wannan daukaka (Wazirin Adamawa) da Allah ya kara  Minista Alhassan ya gabatarwa tsohon mataimakin shugaban kasar shugabannin jam'iyyar, tana mai cewa wasunsu sun matsa domin su yi jawabi a gabansa amma hakan ba zai yiwu ba saboda ya gaji.

Tawagar ta rika yin tafi a lokacin da ministar ke wadannan jawabai.
Ministar ta harkokin mata dai ita ce ta yi takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam'iyyar APC a shekarar 2015, ko da yake ta sha kaye a hannun Gwamna mai-ci, Darius Ishaku na jam'iyyar PDP.

Ya Aka Yi Wannan Sirri Ya Bayyana?



Shakka babu da mamaki Minista ta rika kamfe ga wani saboda ya samu kujerar shugaban kasa da ya ba ta mukami. Shin ba ta yi farin ciki ba ne da mukamin ko kuwa ba ta samun abinda ya kamata da kujerar?

Shin a sirri aka yi wannan abu daga bisani asiri ya tonu? Ko kuwa tana zargin akwai sunanta a Ministoci da za a kora? Shin me ya sa take fatan Atiku ya karbi kujerar Buhari? Su wa suka saki faifan bidiyon?