Showing posts with label Rashawa. Show all posts
Showing posts with label Rashawa. Show all posts
Thursday, 26 October 2017
HARKALLAR FANSHO: Yadda SSS suka dura naira miliyan 152 a asusun Maina
‘Yan sandan Laken Asirin kasar nan, SSS sun taba zurara tsabar kudi a cikin asusun Adulrashid Maina, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.
Hakan ya nuna cewa an dade ana harkalla tsakanin Maina da kuma jami’an SSS. Dama kuma a ranar Alhamis da ta gabata PREMIUM TIMES ta bayyana yadda jami’an na SSS ke ba shi kariya, watakila don kada EFCC su kama shi.
A halin yanzu dai Maina ya cika wandon sa da iska, tun bayan da EFCC suka bayyana cewa suna neman sa, bayan Shugaban Kasa ya bayar da umarnin a kore shi daga aikin da aka maida shi a asirce.
Wani rahoto na musamman da aka gudanar ya tabbatar da cewa Maina ya yi kaurin suna wajen amfani da wani dan’uwan sa ma’aikacin banki mai suna Khalid Ali Biu, ya bude asusun ajiyar kudi da sunan Cluster Logistics Limited a bankin Fedility. An yi wannan harkallar ce a cikin 2011.
Wani abin mamaki shi ne, Khalid ma’aikacin Fedility ne, sannan kuma ya na daya daga cikin daraktocin wannan kamfani na bogi.
Wani bincike kuma ya tabatar da cewa tsakanin 2011 zuwa 2013, an dura zunzurutun kudi a cikin asusun har naira miliyan 500.
Baya ga wanan an kuma gano cewa an rika cirar tsabar kudi ne daga asusun, wadanda akasari duk daloli ne aka rika cira. Sannnan kuma a cikin asusun ne SSS duka dura wa Maina naira milyan 152.
An kuma gano cewa a baya EFCC ta nemi ta boye wannan asarkala da SSS suka yi domin su rufa wa SSS asiri.
Saturday, 14 October 2017
Nigeria: Majalisa za ta binciki asibitin fadar shugaban kasar
'Yan majalisar wakilan Najeriya za su gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da asibitin fadar shugaban kasar ke ciki.
'Yan majalisar sun nuna damuwar cewa duk da irin makudan kudaden da ake ware wa asibitin a kasafin kudin Najeriya , amma ana samun rahoton rashin kayan aiki a asibitin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta zargi asibitin da rashin kayan aiki a makon da ya gabata, lokacin da ta kai ziyara asibitin da ba ta da lafiya.
Hajiya Aisha, ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.
Mai magana da yawun majalisar, Hon Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa, tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar da muke ciki, ana warewa asibitin fadar shugaban kasar kudade a kasafin kudin kasar, dan haka ya ce dole a bincika domin gano inda kudaden suka tafi.
Hon. Namdaz ya ce wani kwamiti na musamman ne aka bawa wuka da naman gudanar da bincike a kan inda kudaden kula da asibitin fadar shugaban kasar suka shiga.
Dan majalisar ya ce nan ba da jimawa ba kwamitin zai fara aikinsa, kuma da zarar ya kammala binciken ya bayar da rahotonsa, za a sanar da jama'ar kasa komai dalla-dalla.
Thursday, 7 September 2017

Yaki da Chin Hanci da Rashawa a Nigeria Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu
Saboda An Wayi Gari a Kasa Irin Nigeria An Samu Kudi an Rasa Mai Su Kowa Na Tsoron Yace Nashi Ne Domin Gudun Hushin Hukuma Wanda A Yan Shekarunan Bamu Taba Tsammanin Haka Zata Faruba
Sai Dai Muyi Godiya Ga Allah Mu Roki Allah Yakara Taimakon Wanan Gwamnatin Wajen Dawo Da Martaban Kasarmu Nigeria
Daga
Aliyu Abdullahi Malumfashi
Subscribe to:
Posts (Atom)