Showing posts with label Kannywood. Show all posts
Showing posts with label Kannywood. Show all posts
Thursday, 26 October 2017
Na tuba, a yafe mini” Rahama ta roki MOPPAN
Shahararriyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Rahama Sadau ta roki kungiyar MOPPAN da ta tausaya mata ta maido ta farfajiyar Fina-finan.
Rahama ta fadi haka ne a wata wasikar tuba da ta rubuta wa kungiyar cewa ta yi nadama kan abinda tayi awancan lokacin.
An kori Rahama Sadau ne daga farfajiyar fina-finan Hausa saboda wani bidiyon waka da tayi da wani mawakin garin Jos mai suna Classique in da ta rungumeshi wanda hakan ya saba wa dokar duk wani dan wasa a farfajiyar Kannywood.
Yanzu dai ta fito fili don rokon a yafe mata.
“Ni halittar Allah ce wanda za ta iya aikata kuskure ko yaushe sannan kuma ni ‘ya ce mai laifi wanda ke shirin gyara abubuwan da nayi ba daidai ba. Ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu MOPPAN, da da masoya na da suyi hakuri da ni su yafe min.
Da gidan jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da Salisu Mohammed, sakataren kungiyar MOPPAN ya tabbatar da mika wasikar hakan ga kungiyar daga Rahama Sadau.
” Lallai Rahama ta mika wa kungiyar wasikar tuba daga abubuwan da ta aikata a baya ga kungiyar da masoyanta, amma duk da haka sai kungiya ta zauna ta duba wasikar da kuma duba irin abubuwan da tayi ta aikatawa da fadi bayan an kore ta game da kungiyar da farfajiyar fina-finan Hausa sannan ta fitar da matsaya daya.
Wednesday, 25 October 2017
Video: Maryam Yahaya Tare Da Hafsat Idris – Bikin Masoya
Sabon video din da ya fita ake tunanin bikin hafsat idris barauniya akayi.
Inda zakuganta tare da wani saurayi da ake tunanin angonta ne suna tika rawa.
Ashe wai shiri ne mai suna gidan biki inda zakuga mayan jarumai kamar haka.
Maryam yahaya, garzali miko, hajara usman, da dai sauransu.
Domin ganewa idanunku kuna iya dakkowa anan shafin kawai Ku shakata da wannan bidiyon.
Download it here
Saturday, 9 September 2017

Hatsaniya ta barke tsakanin Ali Nuhu da Rahama Sadau
Wannan rikicin dai ya far fitowa fili ne sakamakon yadda wasu manya jigogi kuma makusantan jarumi Ali Nuhu din suka fito a kafafen sada zumunta na manhajar Instagram suna aibata jaruma Rahma Sadau da munana kalamai da kuma zagi.
Majiyar much dai ta danyi karamin binciken ta gano cewa musabbabin rikicin bai rasa nasaba da rashin goron gayyata da Ali Nuhu bai ba Rahma Sadau din ba wajen shirya wani sabon fim din sa Abota da ita kuma take ganin kamar ba'a yi mata dai dai ba.
Shi dai Ali Nuhu tamkar wani bango ne a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood inda yake matsayin yaya ko kuma ma uba ga da yawa daga cikin jaruman fim din musamman ma mata.
Haka ma dai mun samu cewa Ali Nuhu din shine musabbanin shigowa da Rahma Sadau harkar fim kuma shine dalilin shaharar ta saboda sanya ta da yayi a cikin wasu fina-finan sa
Source Naij Hausa
Friday, 8 September 2017

Mata uku wadanda suka zamo Sanannu a Arewa na daya zata baka mamaki
Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mata uku sa suka fi tashe a harkar fina-finai da nishadantarwa a yankin mu na arewacin Nigeria
Jaridar Thisday ce dai ta wallafa sunaye gami da hotunan wadannan yan mata a shafinsu na instagram inda suka ayyana su a matsayin manya mata kuma masu tashe a bangaren nishadantarwa a arewa.
Wadannan shahararrun mata dai sune babbar mawakiyar nan Hadiza Blell wacce aka fi sani da suna Dija. Da kuma fitacciyar mai gabatar da shiri a gidan television wato Salma Phillips. Sai kuma jarumar wasan kwaikwayon Hausa Rahama Sadau.
Sunday, 20 August 2017

Yadda Na Ji Rauni A film Din Dakin Amarya —Aisha Tsamiya
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa wakilinmu cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar "Dakin Amarya".
Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama - ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.
"Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin. Kai har kwanciya na yi a asibiti", in ji Aisha Tsamiya.
Jarumar ta kara da cewa tun tana karama take sha'awar fitowa a fina-finan Kannywood "saboda suna matukar burge ni".
A cewarta, "Na dauki yin fim a matsayin sana'a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa."
Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta "kuma ina zaune da kowannensu lafiya".
"Jarumai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni", in ji Aisha Aliyu.
Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.
Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.

Subscribe to:
Posts (Atom)