Saturday 9 September 2017

Home Hatsaniya ta barke tsakanin Ali Nuhu da Rahama Sadau

Subscribe Our Channe



Wannan rikicin dai ya far fitowa fili ne sakamakon yadda wasu manya jigogi kuma makusantan jarumi Ali Nuhu din suka fito a kafafen sada zumunta na manhajar Instagram suna aibata jaruma Rahma Sadau da munana kalamai da kuma zagi.

Majiyar much dai  ta danyi karamin binciken ta gano cewa musabbabin rikicin bai rasa nasaba da rashin goron gayyata da Ali Nuhu bai ba Rahma Sadau din ba wajen shirya wani sabon fim din sa Abota da ita kuma take ganin kamar ba'a yi mata dai dai ba.

Shi dai Ali Nuhu tamkar wani bango ne a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood inda yake matsayin yaya ko kuma ma uba ga da yawa daga cikin jaruman fim din musamman ma mata.

Haka ma dai mun samu cewa Ali Nuhu din shine musabbanin shigowa da Rahma Sadau harkar fim kuma shine dalilin shaharar ta saboda sanya ta da yayi a cikin wasu fina-finan sa

Source Naij Hausa

No comments:
Write comments