Saturday 14 October 2017

Home Crystal Palace ta ba Chelsea mamaki

Subscribe Our Channe




Kungiyar Crystal Palace ta samu nasarar farko a kakar firimiyar bana, bayan da ta doke Chelsea da ci 2-1.

Kungiyar ta yi rashin nasara a duka wasanni bakwai da ta buga a kakar bana - ciki har da guda ukun da ta yi a karkashin jagorancin sabon kocinta Roy Hodgson.

Kuma rabon kungiyar ta zura kwallo a raga tun a watan Mayun da ya wuce.

Nasarar da ta samu ta sa kungiyar ta dan matsa sama daga kasan teburin gasar.

No comments:
Write comments