Sunday, 20 August 2017

Yadda Na Ji Rauni A film Din Dakin Amarya —Aisha Tsamiya

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa wakilinmu cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar "Dakin Amarya".

Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama - ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.
"Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin. Kai har kwanciya na yi a asibiti", in ji Aisha Tsamiya.
Jarumar ta kara da cewa tun tana karama take sha'awar fitowa a fina-finan Kannywood "saboda suna matukar burge ni".
A cewarta, "Na dauki yin fim a matsayin sana'a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa."
Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta "kuma ina zaune da kowannensu lafiya".
"Jarumai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni", in ji Aisha Aliyu.
Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.
Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.

PDP ta lallasa APC a zaben Gombe


Jam’iyyar PDP ta doke APC a zaben cike gurbi da akayi na dan majalisar dokokin jihar Gombe jiya Asabar.Dan takaran kujeran dan majalisar Dukku na jam’iyyar PDP Sa’idu Malala ne ya lashe zaben da kuri’u sama da 7000 in da A Inuwa ya sami kuri’u 4000 da yan kai.

A watan Yunin da ya gabata ne Allah yayi wa dan Majalisar dokokin jihar da ke wakiltan karamar hukumar Dukku Gambo Kabade rasuwa.Jam’iyyu 7 ne suka  takara a zaben.

Saturday, 19 August 2017

Zan sallami Arsene Wenger daga Arsenal idan na siya kungiyar kwallon kafar – Dangote






Hamshakin attajiri, wanda ya fi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa, matsawar ya sayi hannun jarin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Londan, farkon abin da zai fara yi shi ne sallamar mai horas da ‘yan wasa Arsene Wenger.Ya yi wannan bayani ne lokacin da ya ke zantawa da kafar yada labarai mai suna Bloomberg, inda ya kara da cewa, ya nan kan bakan sa na kokarin ganin cewa, da zaran ya kammala ginin matatar man fetur din sa a Legas, zai tuntubi mamallakin kulub din Arsenal, Stan Kroenke, domin sayen kungiyar.


Dangote, wanda darajar arzikin sa ta kai Fam Biliyan 8.6, ya dade ya na goyon bayan Arsenal. Tun cikin shekarun 1980 ya ke dan goyon bayan kungiyar.“Farkon abin da zan fara yi shi ne na sallami mai horas da yan wasan kungiyar. Ya yi rawar gani a tsawon shekarun da ya yi, amma akwai bukatar kawo wani domin shi ma ya jaraba ta sa sa’ar.” Haka Dangote ya shaida wa Bloomberg.Wenger dai ya shafe shekaru 21 ya na koyar da wasan kwallo a kungiyar Arsenal, wanda hakan ya kai shi ga zama wanda ya fi kowane mai horas da wasa dadewa a kungiya daya a kashashen Turai.