Saturday, 14 October 2017
Nigeria: Majalisa za ta binciki asibitin fadar shugaban kasar
'Yan majalisar wakilan Najeriya za su gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da asibitin fadar shugaban kasar ke ciki.
'Yan majalisar sun nuna damuwar cewa duk da irin makudan kudaden da ake ware wa asibitin a kasafin kudin Najeriya , amma ana samun rahoton rashin kayan aiki a asibitin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta zargi asibitin da rashin kayan aiki a makon da ya gabata, lokacin da ta kai ziyara asibitin da ba ta da lafiya.
Hajiya Aisha, ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.
Mai magana da yawun majalisar, Hon Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa, tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar da muke ciki, ana warewa asibitin fadar shugaban kasar kudade a kasafin kudin kasar, dan haka ya ce dole a bincika domin gano inda kudaden suka tafi.
Hon. Namdaz ya ce wani kwamiti na musamman ne aka bawa wuka da naman gudanar da bincike a kan inda kudaden kula da asibitin fadar shugaban kasar suka shiga.
Dan majalisar ya ce nan ba da jimawa ba kwamitin zai fara aikinsa, kuma da zarar ya kammala binciken ya bayar da rahotonsa, za a sanar da jama'ar kasa komai dalla-dalla.
Sunday, 10 September 2017
FYADE: Mata ‘Yan Jarida sun gudanar da zanga-zanga a jihar Filato
Kungiyar ‘Yan Jarida Mata, reshen Jihar Filato sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwar su dangane da yawaitar yi wa mata da kananan yara fyade a kasar nan.
Sun gudanar da wannan jerin-gwano ne a kasuwannin garin Jos, babban birnin jihar Filato.
A jawabin ta, Shugabar Kungiyar ta Jiha, Madam Jennifer Yerima, ta nuna damuwa da matukar takaici ganin yadda ake samun yawaitar yi wa kananan yara fyade, musammam kanana da jirajirai. Ta ce wannan abin takaici ne, abin kunya ne kuma abu ne da al’umma ya kamata gaba daya a tashi tsaye a shawo kan sa. Ta kuma kara da cewa duk alamomin gushewar imani ne daga zukatan mazaje.
Ita kuwa Shugabar Gidauniyar Diamond Support Foundation, Adefunke Agina, wadda da hadin guiwar gidauniyar ta su aka yi gangamin, ta yi kira da a rika zartas da hukuncin kisa kai tsaye ga duk namijin da aka kama ya yi wa mace, karamar yarinya ko yaro fyade.
Ta ce “duk yaro ko yarinyar da aka yi wa fyade, to an fa riga an kassara ta, an tauye mata rayuwar ta kuma har ta mutu abin zai rika damunta a rayuwar su.’
Daga nan sai ta yi kira ga iyayen kananan yaran da aka yi wa fyade su rika fitowa su na fallasawa domin hukuma ta rika daukar mataki.
Ita kuwa Tsohuwar Sakatariyar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Kasa, kira ta yi ga jami’an tsaro da su kara sa ido sosai wajen bai wa rahotanni da koke-koken da suka danganci fyaden mata da kananan yara muhimmanci.
Osinbajo ya nisata kansa da masu yi masa kamfen din fitowa takarar Shugaban kasa
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya nisanta kan sa daga wani kamfen da aka fara yi cewa ya cancanci fitowa takarar shugabancin kasar nan a 2019.
Wata kungiya ce dai da ba ta fito karara ta bayyana kan ta ba, ita ce ta fara yayata wannan kamfen a kafafen sada zumunta a yanar gizo. Sai dai kawai ya ce tushe da hedikwatar kungiyar na can a birnin Belfast, babban birnin kasar Ireland ta Arewa.
Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ne ya nisanta Osinbajo daga wannan kungiya, ya na mai cewa makaryata ne . Ya ce Mataimakin Shugaban Kasa bai taba nunawa ko furtawa cewa zai tsaya takara ba.
Akande ya ce Osinbajo mutum ne mai biyayya ga gwamnati, jam’iyya da kuma shugaba Muhammadu Buhari. Hasali kuma bai ma san da wata kungiya na yi masa kamfen ba.
A karshe ya roki jama’a su yi watsi da kamfen din domin ba da yawun Osinbajo su ke yi ba.
Mutane 19 sun rasa rayukansu a hadarin mota a Kano
Mutane 19 su ka mutu sanadiyyar wani hadarin mota da ya faru a daidai Lambun Garban Bichi, kan hanyar Kano zuwa Katsina.
Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa na jihar Kano, Kabir Daura ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN haka.
Hadarin inji Daura, ya ritsa da fasinjoji 34 wadanda ke cikin mitocin haya biyu, C20 bas da kuma Fijo J5, inda nan take mutane 18 su ka kone kurmus, yayin da na cikon 19 ya mutu a asibitin garin Bichi.
Ya ce sauran fasinjoji 15 kuma sun samu raunuka, kuma aka garzaya da su asibitin garin na Bichi.
Daura ya ce motocin biyu taho-mu-gamu su ka yi. Ya kuma danganta wannan hadari da gudun tsiya, gaggawa da kuma wuce mota a inda doka ta hana direba ya yi aron hannu ya wuce motar da ke gaban sa.
Saturday, 9 September 2017

An daidaita tsakanin malaman Jami'o'i da gwamnatin tarayya
Kungiyar Malaman Jam'i'o'i ta Kasa, ta amince da yarjejeniyar da ta cimma a zamanta da gwamnatin tarayya, inda ta yarda za ta janye yajin aiki da zarar uwar kungiyar ta amince gaba dayan su.
A cimma wannan yarjejeniya ce bayan malaman sun shafe sa'o'i 12 da rabi su na tattaunawa an Abuja.
Har ila yau, a yayin wannan dogon zama da otherwise known as yi, a kuma kafa kwamiti mai kunshe da mutane bakwai a bangaren gwamnati da na bakwai a bangaren malaman Jami'o'in da zu duba yadda gwamnati za ta yi aiki da yarjejeniyar 2009, wacce dama rashin aiki da ita ne ya haifar da yajin aikin.
Kamar yadda Ministan Kwagago, Chris Ngige ya bayyana, ya ce kwamitin zai kunshi wakilai uku daga Ma'aikatar Ilmi, wasu uku daga Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Kasa, sai kuma wakili daya daga bangaren Gwamnartin Tarayya, wanda shi ne zai kasance shugaban kwamiti.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa duk da dai sun amince da yarjejeniyar, za su mika tayin da gwamnati ta yi musu, wurin mambobin su, daga nan bayan sati daya kuma su waiwayi gwamnatin tarayya dangane da matsayar su.
Shugaban kungiyar na kasa, Biodun Ogunyemi, ya shaida wa manema labarai cewa za su koma su tuntubi uwar kungiyar su gaba daya, daga nan kuma bayan mako guda su tunkari gwamnati da abin da su ka zartas.
A nasa bangaren, Ministan Ilmi, Adamu, ya ce a yarda za a biya wa kungiyar bukatun ta, kuma za su janye yajin aiki nan da mako guda bayan sun tuntubi sauran daukacin mambobinsu na fadin kasar nan.
A dai fara tattaunawar damisalin 1:38 na ranar Alhamis, otherwise known as kammala karfe 2:15 na daren Juma'a.
Friday, 8 September 2017

Hotunan sabuwar motor da dan wasan Real Madrid ya siya
Dan wasan Real madrid Cristiano Ronaldo ya samu karuwa cikin jerin motocin da ya tara masu tsada.
Zakaran yan ƙwallon turai ya dora hoton motar wanda kimanin ta ta kai N162M (£350,000) a shafin shi na instagram.
A cikin hoton Cristiano ya tsaya kusa da motar.
Motar kerar Ferarri (Ferarri F12TDf) ne kuma ya shiga cikin jerin motocin da dan kwallon ke da shi.
Cikin jerin motoci masu tsada da dan wasan Real madrid ya tara akwai Porsche 911 Turbo S, Bently GT Speed, Bentley Continental GTC, Ferrari 599 GTB Fiorano, Rolls Royce Phantom Drophead Coupe, Ferrari F430, Koenigsegg CCX da sauransu.
Ya siyo sabon motar bayan ya taimaka ma tawagar yan ƙwallon ƙasar Portugal wajen cin nasara a wasan share fage na buga gasar kofin duniya inda suka gama da kasar Hungary da Faroe Island.
Dan wasan zai koma ga tawagar Real madrid amma ba zai buga wasan su da Levante ranar asabar 9 ga watan Satumba sanadiyar dakatarwa da aka bashi.